Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Abincin da ya kamata a baiwa jarirai

A wani bincike da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi akan lokacin da ya kamata a fara baiwa jarirai abinci, hukumar ta yi gargadin cewa wannan wani lokaci ne da jariri zai iya fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki, muddin ba'a lura ba.

Domin tabbatar da girma da kuma koshin lafiyar jariri, ana so ne a fara bashi wasu nau'o'in abincin daga akalla wata shida, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Har ila yau a wani bincike da sashen abinci mai gina jiki domin lafiya da ci gaba na hukumar lafiya ta duniyar, ya nuna cewa baya ga fara baiwa yaro wasu nau'o'in abincin, ya kamata nonon uwa ya ci gaba da kasancewa babban abinci da jariri zai sha har iya tsawon shekara guda.

Sannan kuma a cikin shekarar jariri ta biyu da haihuwa ya kamata nonon uwa ya kasance daya daga cikin mahimman abincin yaro kafin a kai ga yaye shi, a saboda sinadaran kariyar da nonon uwa ke dashi wanda wasu nau'in abincin ba zasu iya bayarwa ba.

A wani bincike da asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF tare da hadin gwuiwar hukumar lafiya ta duniya WHO, binciken ya bayyana cewa a lokacin da aka fara baiwa yaro wasu nau'o'in abinci, ya kamata ya kasance mai ruwa ruwa, sai kuma daga baya a fara bashi mai dan karfi kadan kadan.

Shirin mu kenan na wannan makon. Ayi sauraro lafiya.