Ana zaman dar-dar a Jos

Wani sabon tashin hankali ya barke a Jos, babban birnin jihar Filato.

Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne a Unguwar Dogon Karfe da kuma Abbatoire.

An ce, an ga mutane dayawa da aka jikkata da bindiga. Rahotanni na kuma cewa, ana ci gaba da samun kisan dauki daidai a birnin na Jos, tun bayan da aka samu tashin hankali a ranar Litinin da ta gabata, tsakanin Krista da Musulmi, inda jami'an tsaro suka ce fiye da mutane sha ukku sun hallaka.