'Yan tawaye na kokarin killace Sirte

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Dakarun 'yan tawaye a Libiya na ta kokarin killace birnin Sirte, wanda shine yanki mafi girma da ke goyon bayan Kanar Gaddafi.

An ce, 'yan tawayen suna bude wani fagen dagar daga Kudu.

Majalisar Wucin Gadin Libiyar ta ba mazauna birnin wa'adin nan da ranar Asabar, na su mikan kansu.

Sai dai a cewar kakakin Kanar Gaddafi, ba za su amince da hakan ba, daga mutanen da ya bayyana da cewa: karnuka masu dauke da makamai.