'Yan tawayen Libya sun shiga Turabulus

Hakkin mallakar hoto AP

Daruruwan dakarun 'yan tawayen Libya sun shiga babban birnin kasar inda suka yi ta raye-raye don bayyana farin cikinsu.

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta Duniya ta tabbatar cewa an kama dan shugaba Gaddafi, Saif al-Islam.

Kazalika kakakin gwamnatin Libya, Moussa Ibrahim, ya ce fiye da mutane 1, 300 ne 'yan tawayen suka kashe a yunkurin da suke yi na shiga Turabulus.

Wani hafsan soji a bangaren 'yan tawayen ya ce yana da muhimmanci su isa birnin Turabulus din don taimakawa tada kayar bayan da ake yi a can.