'Yan tawaye sunce sun kusa kame Tripoli

'Yan tawayen Libya

'Yan tawaye a Libya na ci gaba da rike wuraren da suka kame, yayinda suke ci gaba da kokarin dannawa zuwa Tripoli, babban birnin kasar.

Wata sanarwar talabijin da 'yan tawayen suka yi ta bukaci mazauna birnin da su zauna cikin shirin isar su

'Yan tawayen sun ce sun kame tsakiyar garin zawiya, kuma sun ce yanzu su ne ke iko da birnin Brega mai matukar muhimmanci.