An gano baban Mikel Obi

Rundinar 'yan sanda a jihar Kano a Najeriya ta ce ta yi nasarar kubutar da mahaifin shahararren dan wasan kwallon kafar nan dake bugawa kulob din Chelsea, wasa, John Mikel Obi.

Rundunar tace ta kubutadda shi ne bayan wani samamen hadin gwiwa da suka kai kan wani gida da ke birnin Kano.

An sace Michael Obi ne kwanaki goma da suka ce, bayan da ya tashi daga aiki a birnin Jos na jihar Pilato.

Yan sandan sun kama mutane shidda a lokacin samamen.