Ambaliya ta hallaka mutane a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumomi a jihar Oyo dake Kudu maso Yammacin kasar sun ce akalla mutane 20 ne suka rasa rayikansu, wasu karin dubbai kuma suka fice daga muhallinsu, a sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a birnin Ibadan.

Sun ce ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwariya a ranar Jumaa, ya janyo cika da kuma batsewar wani dam, abun da ya sa ruwan suka yi awon gaba da gine-gine da kuma gadoji.

Yanzu haka dai, an tsugunnar da mutanen da suka rasa muhallinsu a wasu sansanoni.