An kashe wasu 'yan sanda uku a Maiduguri

Wasu 'yan sandan Najeriya
Image caption Wasu 'yan sandan Najeriya

'Yan sanda a Arewaci Nijeriya sun ce wasu da ake kyautata zaton 'yan wata kungiyar kishin Islama mai gwagwarmaya da makamai ce sun kashe wasu 'yan sanda uku da wani farar hula.

Mutanen na kallon talabijin a gidan daya daga cikinsu, lokacin da 'yan bindigar suka afka ciki suka bude musu wuta a birnin Maiduguri na jihar Borno.

'Yan sanda sun dora laifin kisan a kan kungiyar da aka fi sani da suna , Boko Haram, wadda a baya ta amsa kashe jami'an tsaro, da wasu shugabannin al'umma da ma malaman addini, a birnin na Maiduguri da wasu sassan na Arewacin Nijeriya.