Mutane 40 sun mutu a Pakistan

Masallacin Hakkin mallakar hoto AFP

Wani bam da ya tashi cikin masallaci, yayinda ake sallar juma'a a Pakistan ya hadasa mutuwar mutane sama da arba'in.

Wasu mutane akalla tamanin sun jikkata a harin, wanda aka kai a lardin Khyber na arewa maso yammacin kasar.

Arshad Khan wanda ke cikin masalacin lokacin da abin ya faru ya ce;.

"Akwai mutane kimanin dubu daya da dari biyu zuwa dubu daya da dari uku a cikin masallacin."

" Daga nan sai mun ka ji an ce, Allahu Akbar, allah Mai girma, daga nan sai bam ya tashi."

Wani wakilin BBC ya ce hare haren baya da ake kaiwa a yankin na Khyber ana kai su ne a masallatai, domin a kashe jama'a masu dimbin yawa.

Yankin yayi kaurin suna wajen rikici tsakanin kungiyoyin mayaka masu gaba da juna.