Syria ta yi watsi da kiran Amurka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Garin Latakia a Syria inda hayaki ke tashi

Syria ta yi watsi da kiranda Amurka da kawayenta suka yiwa shugaba Bashar al-Assad da yayi murabus, da cewa abin kunya ne, kuma haramtacce.

Jakadan kasar Syria a Majalisar dinkin duniya Bashar Ja'afari, ya zargi Amurka da kokarin ruruta rikicin kasarsa.

A gobe Asabar ne dai, ake sa ran Majalisar dinkin duniya za ta aike da wakilai daga hukumar jin kai na majalisar, zuwa Syria.

Ta ce, an yi mata alkawarin cewa, za a baiwa wakilan na ta damar shiga ko ina.

Bayaga kiran da tayi ma shugaba Asad kan ya sauka daga mulki, Amurka ta yi shellar dakatar da amfani da kadarorin Syria dake kasar kuma ta sanyawa masana'antar makamashin kasar takunkumi.

Wanan dai wani babban yunkuri ne sai dai ba zai yi wani tasirin kirki ba idan be samu goyon bayan kasashen turai ba wadanda ke sayen kashi casain cikin dari na albarkatun mai na Syria.

Sai dai matsin lambar na karuwa kuma a kwanaki masu zuwa Birtaniya da sauran kasashen turai zasu zartar da wani daftarin doka da zai bayana irin takunkumin da za'a sanyawa kasar.