Turkiyya za ta ajiye jakada a Somalia

Mr Tayyip Recep Erdogan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Tayyip Recep Erdogan

Praministan Turkiyya , Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyara Mogadishu, babban birnin Somaliya--inda yayi alkawarin bude ofishin jakadanci, domin taimakawa wajen raba kayan agaji ga wadanda fari ya shafa a kusurwar gabashin Afrika

Mr Erdogan ya kuma ce Turkiyya za ta sake gina hanyar zuwa filin jirgin saman Mogadishu, da gyara asibiti, da kuma gina makarantu da rijiyoyin burtsatse.

Ranar Laraba, ya jagoranci taron kasashen Musulmi, inda aka tara dala miliyan dari uku da hamsin ga Somaliar.

Mr Erdogan dai shi ne wani shugaban siyasa na farko daga wajen nahiyar Afrika, da ya kai kai kasar ta Somalia a cikin shekaru 20 din da suka wuce.