Masar ta janye jakadan kasar daga Israila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu jami'an sojin Masar

Majalisar zartarwa ta Masar ta ce ta yanke shawarar janye jakadanta daga Israila dangane da mutuwar jamian tsaron Masar, bayan wani harin da Israila ta kai a kusa da iyakar kasashen biyu.

A bangare guda kuma daruruwan yan kasar Masar sun gudanar da zanga zanga a wajen ofishin jakadancin Israilar dake birnin Alkahira inda suka kona tutar Israilar .

Gwamnatin Masar tace zata janye jakadan kasar har sai gwamnatin Israilar ta gudanar da bincike akan mutuwar jamian tsaron masar su biyar.

Sai dai rundunar sojin Israilar tayi alkawarin gudanar da bincike akan batun.

Sanarwar ta kuma ce israila itace keda alhakin kai hare haren a siyasance inda ta ce abun da ya faru ya sabawa yajejeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Tuni jakadan Israila a Masar ya bayana a gaban ofishin ma'aikatar harkokin wajen kasar domin su kara tattaunawa akan wannan batu.