Kungiyar larabawa zata yi taron gaggawa a yau

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wani wuri da aka kaiwa hari a zirin Gaza

Mataimakin shugaban kungiyar hadin kan larabawa Ahmed Ben Helili ya ce zasu gudanar da taron gaggawa a yau lahadi domin su tattauna akan halin da a ake ciki a zirin Gaza bayan jerin hare haren da Israilar ta kai da jiragen sama da ya kashe Palasdinu da dama.

Yace taron ya biyo bayan koken da palasdinu suka gabatarwa kungiyar inda suka nemi a ayi nazari akan ilolin da wanan yanayi me hadari zai janyo biyo ayan harin da Israilar ke cigaba da kaiwa zirin Gaza.

A dayan bangaren sojojin Israilar da mayakan Palasdinu sun yi artabu a jiya asabar inda rokokin da aka harba daga zirin Gaza sun sa wasu ma'aikatan palasdinu su uku dake aiki a kudancin Israilar sun samu raunuku , kana jiragen saman israilar sun kaima gabar tekun zirin Gaza hari.

Rundunar sojin israilar tace rokoki goma sha tara ne suka fado cikin kasar da safiyar jiya sai dai tace bayan harin da aka kaiwa garin Ashdod babu wani wurin da mutane suka jikkata.

Hakan na zuwa a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar rikici a fanin diplomasiya yayinda dubun dubatar mutane ki cigaba da halara a wajen ofishin jakadancin kasar dake birnin al'qahira inda suka rika yin kira a kori jakadan Israilar daga kasar.