Ana ci gada da fada a Tripoli

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan tawayen Libya

'Yan tawayen Libya na ci gaba da gwabza fada da sojoji masu biyayya ga Kanal Gaddafi don kwace iko da birnin Tripoli.

'Yan tawayen sun ce sun kwace sassa da dama na birnin, amma suna fuskantar turjiya sosai a wasu bangarorin birnin.

Dakarun 'yan tawayen sun tudada cikin birnin Tripoli ne a daren jiya kuma suka kwace iko da babban dandalin birnin inda dubban mazauna birnin suka hadu da su domin murna

Gwamnatin Kanar Gaddafi ta zargi 'yan tawayen da kashe fiye da mutane dubu da dari uku.

Ta ce kungiyar tsaro ta NATO ce ta tallafawa 'yan tawayen wajen gudanar da kashe-kashen.

Sai dai kungiyar ta musanta zargin inda ta ce 'yan tawayen sun gudanar da ayyukansu ne kawai don kishin kasa.

Shugabannin kasashen duniya da dama dai sun yi kira ga Shugaba Gaddafi ya sauka daga mulki tun lokaci bai kure masa ba.

Muhimman yankuna a birnin Turabulos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani