A yau za'a rufe bikin matasa ta duniya

Image caption Paparoma Benedict

Paparoma Benedict, zai kaddamar da bukin rufe ranar matasa ta duniya, cikin sa'oi kalilan dake tafe a wani sansanin sojin sama dake wajen birnin Madrid.

Bukin ya janyo dubun dubatar masu ziyara daga sassan duniya da dama zuwa babban birnin kasar ta Spaniya.

A jiya Asabar ne dai, wata tsawa mai karfin gaske ta yiwa jawabin na Paparoma cikas inda iska ta dauke hularsa, sannan ruwa ya jika takardar da yake karantawa.

To saidai bayan ruwan, Paparoman ya shaidawa cincirindon mutanen cewa ruwan saman, albarka ne, bayan zafin da aka yi a ranar.