Wakilan Majalisar dinkin duniya sun isa Syria

Wakilan Majalisar dinkin duniya sun isa Syria, don yin nazari game da halinda alummar kasar ke ciki, yayinda dakarun gwmanatin kasar ke ci gaba da daukar matakan soji kan masu zanga zanga.

An shaidawa tawagar wakilan, cewa za su iya shiga dukkanin inda ake fama da rikicin a Syria.

To saidai wakilin BBC a gabas ta tsakiya, ya ce akwai alamar tambaya game da damar da za a iya ba su ta shiga ko ina, da irin abubuwanda za a bari su gani.