Karin matsin lamba kan Kanal Gaddafi

Karin matsin lamba kan Kanal Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban 'yan tawaye Mustafa Abdul Jalil

'Yan tawayen Libya na kara matsa kaimi kan birnin Turabulus, bayan da suka kaddamar da hari kan birnin a daren Litinin - yanzu sun kame 'ya'yan Kanal Gaddafi uku.

Kwamandojin 'yan tawayen sun ce a yanzu suna rike da kashi 80 cikin dari na birnin, ciki harda babban ofishin gidan talabijin na kasar.

Ana kuma ci gaba da gwabza fada a kewayen gidan Kanal Muammar Gaddafi, sai dai babu tabbas ko yana birnin na Turabulus ko kuma ya fice.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa ana ci gaba da gwabza fada a kusa da kan iyakar Libya da Tunisia.

A yanzu ana ci gaba da tattaunawa tasakanin kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da kuma 'yan tawayen Libya, kan yiwuwar mika dan kanal Gaddafi Saiful Islam wanda kotun ke tuhuma.

An kame Saiful Islam ne tare dan uwansa Muhammad bayan da 'yan tawaye suka shiga birnin Turabulus. Rahotanni sun kuma ce an kara kame wani dan na Kanal Gaddafi al-Sa'ad Gaddafi .

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan tawaye ne keda iko da sassa da dama na birnin Turabulus

Matin lamba na karuwa

Shugabannin kasashen duniya sun nemi Gaddafi da ya yi murabus, kuma Masar ta amince da 'yan tawayen a matsayin halartattun wakilan jama'ar Libya.

Wasu daga cikin kasashen Larabawa da na Afrika sun fara nuna goyon bayansu ga Majalisar riko ta 'yan tawayen.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana goyon bayan al'ummar Libya, bayan da 'yan tawaye suka kame mafi yawan sassan turabulos babban birnin kasar.

"Muna goyon bayan abin da jama'a suke so, muna kuma kira da a tabbatar da doka da oda a Libya, a cewar Olubenga Ashiru, ministan harkokin wajen Najeriya.

Masarautar Abu Dhabi ta taya shugaban Majalisar riko ta 'yan tawaye murnar nasarar da suka samu a kutsen da suke yi a birnin na Turabulus.

Taswirar 'ya'yan Kanal Gaddafi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shi ma Sa'ad Gaddafi yanzu yana hannun 'yan tawaye

Karin bayani