Yunkurin kame birnin Turabulos na Libya

Ana ci gaba da gwabza fada a birnin Turabulos na kasar Libyaya, bayan da 'yan tawaye suka kutsa kai tsakiyar birnin, inda suka kame 'ya'yan Kanal Gaddafi biyu.

Magoya bayan yan tawayen dauke da makamai sun yayyaga tutocin kasar da kuma hotunan kanal Gaddafi.

Mai magana da yawun 'yan tawayen ya ce suna saran karbe iko nan da 'yan kwanaki kadan , sannan ya nemi a kwantar da hankali.

Ana kuma ci gaba da tattaunawa tasakanin kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da kuma 'yan tawayen Libya, kan yiwuwar mika dan kanal Gaddafi Saiful Islam wanda kotun ke tuhuma.

An kama shi ne tare da dan uwansa Muhammad lokacin da 'yan tawaye suka shiga birnin na Trabulos.

Har yanzu dai babu tabbas kan ko'ina Kanal Gaddafi ya ke a birnin na Trabulos.

Tsohon mataimakinsa Abdessalem Jalloud, ya ce ba ya tunanin Gaddafi zai mika wuya ko kuma ya kashe kansa.