An sallami tsohon shugaban Asusun IMF

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dominique Strauss-Kahn

Kotu a birnin New York ta yi watsi da zargin da ake wa tsohon shugaban asusun bada lamunin IMF, na yiwa wata mata fyade.

Masu gabatar da kara sun ce, ba za su iya bada shaidar da zata karyata furucin da Dominique Strauss-Kahn yayi ba, cewa abinda ya faru tsakaninsa da Nafissatou Diallo, wata mai aikace-aikace a hotel, da yardar ta ne.

Lauyoyin Nafissatou Diallo sun daukaka kara, suna neman a nada sabbin masu shigar da kara.

To amma sai nan da nan wata kotu ta yi watsi da bukatar.

A yanzu kenan Dominique Strauss-Kahn ya sami kanshi