Kazamin fada a kusa da fadar Kanal Gaddafi

Gaddafi
Image caption Kanal Gaddafi ya shafe shekaru 42 yana mulki a Libya

Ana gwabza kazamin fada a sassan birnin Tripoli na kasar Libya, inda 'yan tawaye ke maida hankali a kusa da fadar Kanal Muammar Gaddafi wato Bab al-Azizya. Gundumar al-Mansoura nan ne aka fi gwabza fada tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da 'yan tawaye suka kutsa kai birnin Tripoli, inda jama'a suka fito domin maraba da su.

Sai dai dakarun Gaddafi na ci gaba da kai hare-hare da manyan makamai, abinda ya sanya shakku kan ikirarin 'yan tawayen na cewa suna rike da mafi yawancin birnin.

Wakilin BBC Matthew Price a birnin Tripoli ya ce ana ganin hayaki na tashi a kusa da fadar Kanal Gaddafi. Amma har yanzu babu tabbas kan inda Gaddafin ya ke.

"Daga dukkan alamu fada bai kare ba. Birnin na cikin halin rashin tabbas," a cewar wakilin gidan talabijin na Al Jazeera James Bays.

Saif al-Islam ya bayyana

A kwai rahotannin da ke cewa jiragen yakin Nato na shawagi kasa-kasa a kan fadar Kanal Gaddafi ta Bab al-Azizya.

A wani lamari mai ban mamaki, Saif al-Islam, dan Kanal Gaddafi, wanda ake kyautata zaton cewa shi ne zai gaje shi ya bayyana a birnin Turabulus a ranar Talata inda ya musanta ikirarin da 'yan tawayen Libya suka yi cewa sun kama shi.

Shi dai Saif al-Islam na cike ne da alfahari inda ya shaidawa BBC cewa dakarun gwamnati sun karya lagon 'yan tawayen bayan da suka yi musu kofar rago.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif aI-Islam yana ganawa da 'yan jarida

Ya jaddada cewa mahaifin sa, Kanal Gaddafi, na nan a Turabulus cikin koshin lafiya.

Ya ce kungiyar tsaro ta NATO ce kawai ke yada karairayi game da kamun na sa, amma a zahiri babu abin da ya same shi.

'Za mu koma Turabulus'

A yayin da ake ci gaba da dauki- ba- dadi na neman kwace iko a Turabulus, shugabannin 'yan tawaye sun ce sun yi shirin komawa birnin a gobe Laraba don kama aiki gadan- gadan na kafa sabuwar gwamnati.

Sai dai jagoran 'yan tawayen, Mustafa Abdel Jalil, ya ce matakin da ake ciki na da hadarin gaske saboda magoya bayan Kanal Gaddafi ka iya kai hare-haren ramuwar gayya.

Ya yi barazanar ajiye aiki matukar kwamandojin 'yan tawayen suka ki yin biyayya ga ka'idojin yakin da suke yi da gwamnatin Gaddafi.

Muhimman wurare a birnin Tripoli

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani