Majalisa ta damu game da rikicin Sudan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ban Ki- Moon

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa game da tashe-tashen hankulan kabilanci da suka barke a makon jiya a jihar Jonglei da ke Sudan ta Kudu inda fiye da mutane dari shida suka mutu.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta ke ziyara a kasar ta ce kusan mutane dubu daya ne suka jikkata a rikicin.

Wakililiya ta musamman ta Sakatare Janar na Majalisar, Hilde Johnson, ta yi kira ga bangarorin da ke fada da juna da su yi taka-tsantsan, inda ta ce a shirye Majalisar Dinkin Duniya take wajen ganin an sasanta dukkan bangarorin.

A watan jiya ne dai Sudan Ta Kudu ta samu 'yancin kai bayan ta shafe kusan shekaru hamsin tana yaki da kasar Sudan.