An kama wasu sojoji kan sace Michael Obi

A Najeriya rundunar sojin kasar ta tabbatar da cewa akwai jami'anta biyu a cikin mutanen da ake zargi da sace mahaifin, John Mikel Obi, dan kwallon Najeriya, da kuma kulob din Chelsea na Ingila.

Da ma dai Michael Obi, wanda rundunar 'yan sandan Najeriya ta kubutar jiya Litinin a Kano, bayan sace shi da aka yi fiye da mako guda da ya wuce, a garin Jos na jihar Plateau, ya yi zargin cewa cikin wadanda suka sace shi har da jami'an sojin Najeriyar.

Rundinar sojin ta ce a yanzu tana tsare da jami'anta biyu da ake zargi, inda kuma take gudanar da bincike kan lamarin.