Saif al-Islam ya bayyana a Turabulus

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif al-Islam a lokacin da ya bayyana a Turabulus

Saif al-Islam, dan Kanal Gaddafi, wanda ake kyautata zaton cewa shi ne zai gaje shi ya bayyana a birnin Turabulus a jiya Talata inda ya musanta ikirarin da 'yan tawayen Libya suka yi cewa sun kama shi.

Shi dai Saif al-Islam na cike ne da alfahari inda ya shaidawa BBC cewa dakarun gwamnati sun karya lagon 'yan tawayen bayan da suka yi musu kofar rago.

Ya jaddada cewa mahaifin sa, Kanal Gaddafi, na nan a Turabulus cikin koshin lafiya.

Ya ce kungiyar tsaro ta NATO ce kawai ke yada karairayi game da kamun na sa, amma a zahiri babu abin da ya same shi.

'Za mu koma Turabulus'

A yayin da ake ci gaba da dauki- ba- dadi na neman kwace iko a Turabulus, shugabannin 'yan tawaye sun ce sun yi shirin komawa birnin a gobe Laraba don kama aiki gadan- gadan na kafa sabuwar gwamnati.

Sai dai jagoran 'yan tawayen, Mustafa Abdel Jalil, ya ce matakin da ake ciki na da hadarin gaske saboda magoya bayan Kanal Gaddafi ka iya kai hare-haren ramuwar gayya.

Ya yi barazanar ajiye aiki matukar kwamandojin 'yan tawayen suka ki yin biyayya ga ka'idojin yakin da suke yi da gwamnatin Gaddafi.