Za a binciki Syria kan tauye hakki

Kwamitin kare hakkin jama'a na majalisar dinkin duniya, ya bada umurnin a gudanar da cikakken bincike, mai zaman kansa, akan zarge-zargen taka hakkin bil'adama a Syria.

A karshen taron gaggawar da yayi, kwamitin yayi Allah wadai da hare-haren da dakarun tsaron Syria ke kaiwa masu zanga zanga - hare haren da majalisar ta ce sun janyo hallakar akalla mutane dubu biyu da dari biyu.

Jakadan kasar Poland a majalisar ya ce, sun yi amannar wannan kudurin, martani ne karara da kwamitin ya mayar ga lamarin keta hakkin bil'adama a Syria.

Rasha da China sun kada kuri'ar kin amincewa da kudurin, wanda suka ce ya nuna son-kai, kuma an sa siyasa a ciki.

Abin da ba a sani ba, shi ne ko hukumomin Syria zasu bada hadin-kai ga masu binciken majalisar dinkin duniyar.