Takaddama ta kaure a jihar Filato

Image caption Gwamnan Filato, Jonah Jang

Al'ummar Hausawa da Fulani da ke jihar Filato a Najeriya sun zargi gwamnatin jihar da nuna musu wariya inda ta ki daukar mambobinsu aiki a rundunar tsaro ta musamman da ta kafa.

Gwamnatin jihar dai ta kafa rundunar ce, wacce ta ce za ta kunshi jami'an tsaro da kuma al'umomi daban-daban na jihar, da zummar wanzar da zaman lafiya.

Sai dai shugaban kungiyar Jasawa da ke kare hakkin Hausawa da Fulani a jihar, Shehu Ibrahim Masalla, ya ce gwamnati ba ta sanya al'umarsu a cikin rundunar ba.

Amma Babban Jami'in tsare-tsare na rundunar, Bala Danbaba, ya ce suna jiran majalisar dokokin jihar ce ta zartar da dokar da za ta bayar da damar daukar mutane aiki a rundunar.