Kamfanin mai na Tullow zai bunkasa hakar mai a Ghana

Kamfanin Tullow Oil dake da mazauni a birnin Landan ya sanar da cewa, zai kashe akalla dala biliyan hudu don bunkasa yankunar hakar mai da ke gabar tekun Ghana.

Kamfanin na Tullow dama yana gudanar da harkokinsa a kasashen Ghana, gabon da Ivory coast.

Wakilin BBC ya ce wajen hakar mai na Jubilee da ke Ghana shi ya fi dukkansu ci gaba.

Yana samar da gangar mai dubu saba'in da biyar a kowacce rana, kuma yana samar da kudin shiga da ya kai kimanin dala miliyan dubu daya ga kasar ta Ghana a kowacce shekara.

Babban jami'in kamfanin na Tullow, Aidan Heavy ya ce suna tattaunawa da gwamnatin Uganda domin kafa wata matatar mai, wacce ka iya baiwa sabuwar kasar sudan ta kudu damar fitar da manta ba sai ta bi ta kasar Sudan ba.