Tattaunawa kan batun nukiliyar Koriya ta Arewa

Shugaba Medvedev da Kim na Koriya ta Arewa
Image caption Wannan ce ziyara ta farko da shugaba Kim ya kai Rasha a shekaru 10

Koriya ta Arewa ta ce za ta sauya tunani kan shirinta na nukiliya, bayan da shugaba Kim ya yi ganawar keke-da-keke da shugaba Medvedev na kasar Rasha.

Wata mai magana da yawun shugaban Rasha ce ta bayyana haka, bayan tattaunawar da shugabannin biyu suka yi a gabashin Siberia game da hadin kan tattalin arziki da kuma yiwuwar komawa ga tattaunawar bangarori 6.

Mr Kim ya tafi Rasha ne ranar Asabar - a ziyararsa ta farko a can a cikin kusan shekaru 10 bayan alamun cewar tsaikon harkokin diflomasiyya a kan mashigin ruwan Koriya na ingantuwa.

Ganawar wadda ba kasafai ake irinta ba a kasar ta Rasha, ta biyo bayan makwanni da aka shafe ana sabuwar tattaunawa tsakanin wakilan kasar Koriya ta arewa da na Kudu da kuma na Amurka.

Domin lalubo hanyoyin da za a bi wajan komawa tattaunawa kai tsaye kan shirin nukuliyar Koriya ta Arewan.

Koma bayan tattalin arziki

Sai dai wannan wata dama ce ta tattauna alakar tattalin arziki da ke tsakanin Koriya ta Arewa da makotanta na gabaci.

An ruwaito mai magana da yawun shugaban Rashan tana cewa, ya amince cewa za a iya cimma yarjejeniyar gina bututun mai da zai bi ta cikin kasar Koriya ta Arewan zuwa makociyar ta Koriya ta kudu wadda ke yunwar makamashi.

Wannan yarjejeniya ce da kamfanin iskar Gas na kasar Rasha Gazprom ke aiki a kai tun tsawon shekaru da dama da suka gabata.

Koriya ta arewa ta ci gaba da daga murya kan bukatar a taimaka mata da zuba jari, don farfado da tattalin arzikinta dake kokarin durkushewa.

Yayin da ake yada jita-jitar cewa Mr Kim bai samu yadda yake so ba a ziyarar da ya kai kasar China a kwanakin baya, masu fashin bakin siyasa na ganin akwai yiwuwar yana neman taimako ne a daya kasar da ke goya masa baya.