Karar da salami ya shigar ta fara fuskantar koma baya

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Mai shari'a Ayo Salami

A Najeriya shari'ar da aka shirya fara yi kan karar da tsohon shugaban Kotun daukaka kara ta kasar mai shari'a, Ayo Salami ya shigar, ta fara fuskantar koma baya, bayan da kusan baki dayan wadanda ake kara ba su samu halartar zaman kotun ba.

Mai shari'a Salami ya je kotun ne domin bukatar ta yi watsi da rahoto da kuma matakin da hukumar kula da harkokin shari'a ta kasa NJC ta dauka na dakatar da shi.

Ko a ranar talata ma, Mr Salami ya shigar da wata karar inda yake neman kotun da ta yi watsi da matakin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya dauka na nada sabon shugaban kotun na wucin gadi.

Duk da cewa wannan ne zama na farko domin share fage, kafin fara shari'ar gadan-gadan, alamu sun fara nuna cewa za a kai ruwa rana.

Cikin mutane 11 da mai shari'a Ayo Salami yake kara, wadanda suka hada da hukumar NJC da kuma mabobin kwamitinta na zartarwa da suka dauki matakin dakatar da shi, da kuma neman shugaban kasar da ya yi masa ritaya, daya ne kacal ya samu wakilci a kotun, wato hukumar NJC, wacce ita ma ainahin lauyanta baije ba, sai wakili ya tura.

Lauyan da ke kare Ayo Salami, Barista Oluyumi, ya shaida wa kotun cewa sun gabatar da sammacin ga Hukumar ta NJC, amma ta ce nata sammancin kawai za ta karba, abinda kuma yasa sai hudu daga cikin wadanda ake karar kawai suka iya kaiwa sammacin.

Daga nan ne kuma ya nemi kotun data basu ikon lika takardun sammacin a ginin hukumar ta NJC, bukatar da kotun taki amincewa da ita, tana mai cewa mutanen ba su nuna alamun kauracewa shari'ar ba tukunna.

Kotun ta umarci da a gabatar da sammaci ga duk wadanda ake kara, kafin ranar 7 ga watan Satumba, inda daga nan ne za ta san mataki na gaba.