Ana son sanyawa Syria takunkumi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bashir al-Assad

Kasashen da ke kungiyar Tarayyar Turai tare da goyon bayan Amurka sun ce sun shirya gabatar da wani kudiri ga Majalisar Dinkin Duniya da ya nemi a sanyawa gwamnatin Syria takunkumi.

Jami'an diflomasiyya na Faransa sun ce ana rarraba daftarin kudirin ga mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Kasar Rasha, wacce ke da kuri'a a kwamitin tsaron, ta ce lokaci bai yi ba da za a sanyawa Shugaba Assad takunkumi.

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva ta bukaci a gudanar da bincike kan rikice-rikicen da suka sanya jami'an tsaron Syria amfani da karfi a kan masu zanga-zanga.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce an kashe fiye da mutane dubu biyu sakamakon hare-haren da jami'an tsaron suka kaiwa jama'a a kasar.