An kashe auren wasu 'yan madigo biyu a Indonesia

Ana yiwa wata mata hukuncin bulala a Aceh Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yiwa wata mata hukuncin bulala a Aceh

'Yan sandan musulunci a lardin Aceh na Indonisia, sun tilasta wa wasu 'yan madigo biyu da ke auren juna rabuwa, suka kuma rusa auren, duk da cewa madigo ba laifi ba ne a dokar kasar ta Indonisia.

Wasu makotan matan ne suka ankarar da 'yan sanda bayan sun tsargu da su, daya daga cikinsu ta gabatar da kanta a matsayin namiji a lokacin aurensu.

Lardin Aceh, shi ne kadai lardin da ke aiki da tsarin shari'ar Musulunci a kasar ta Indonisia.

A shekaru biyu da suka gabata majalisar dokokin yankin ta zartar da dokar da za ta bada damar a yi wa 'yan madigo bulala, amma gwamnan Aceh ya ki ya sanya wa dokar hannu.