Shugaban kamfanin Apple ya ajiye mukaminsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Steve jobs

Daya daga cikin mutanen da suka kafa kamfanin da ke kera na'urorin sadarwar nan na Apple, Steve Jobs ya sauka daga mukaminsa a matsayin shugaban kamfanin.

Mista Jobs ya sanya kamfanin na Apple ya kasance daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a duniya a lokacin shugabancin sa, inda a lokacin ne aka samar da na'urorin sadarwa irin su Ipod, da IPhone.

Da ma dai Mista Jobs ya dauki hutu daga kamfanin inda ya ke jinyar cutar dajin da ya ke fama da ita.

Mista Tim Cook, wanda shi ne babban jami'in gudanarwa na kamfanin ne dai zai maye gurbinsa.