'Yan sanda sun yi karin haske kan harin da aka kai a Gombi

Wasu 'yan sandan Najeriya
Image caption Wasu 'yan sandan Najeriya

Rundinar 'yan sandan jihar Adamawa a Najeriya ta yi karin haske kan harin da wasu 'yan bindiga da baa san ko su wanene ba suka kai kan Ofishin 'yan sanda da wasu bankunan biyu dake garin Gombi a jiya.

A wani taron manema labarai da ta kira yau a Yola, rundinar 'yan sandan ta ce mutane 16 ne suka rasa rayikansu a hare-haren, ciki har da fararen hula 8 da 'yan sanda 7 da kuma dan bindiga 1.

A wata hira da BBC, kakakin rundinar 'yan sandan jihar ta Adamawa, Mrs Altine Daniel ta ce sun yi nasarar kwace motoci biyu na maharan, da kuma makamai da harsasai da dama.

Ta kara da cewa yanzu haka 'yan sanda na cikin jeji suna farautar maharan, wadanda ta bayyana da cewa barayi ne.