Harin bam a Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja

Hakkin mallakar hoto nta
Image caption Akalla mutane sittin ne su ka jikkata a harin bam din

A Najeriya, wata mota dauke da bam ta kai hari a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha takwas.

Tashin bam din dai ya lallata hawa daya na ofishin, inda bam din ya jikkata akalla mutane sittin.

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, ya shaidawa BBC cewa a watan daya gabata, sun samu bayanan sirri da ke nuni da cewa, 'yan kungiyar nan ta Boko Haram za su kai hari ofishin Majalisar.

An dai tsarara matakan tsaro a babban birnin na Abuja.

A watan Yuni ma sai da aka kaddamar da harin bam da mota a hedkwatar 'yan sanda dake Abuja, harin kuma da aka alakanta ga kungiyar nan ta Boko Haram.

Tuni dai Kungiyar Boko Haram ta dau alhakin kaddamar da harin.

Wadanda su ka gani da ido dai sun ce wata mota ce ta shiga ofishin da karfin gaske inda ta balla kofar shiga harabar ofishin Majalisar.

Gwamnatin Najeriya ta Allah-wadai da hari

Minista a Ma'aikatar harkokin wajen Nigeria, Viola Onwuliri, wadda ta ziyarci ginin na Majalisar Dinkin Duniya inda bomb din ya tashi, ta ce gwamnatin Nigeria ta yi Allah wadai da wannan hari.

Ministar ta ce hari a kan ginin Majalissar duniya, hari ne ga daukacin al'ummar duniya.

Ministar ta kara da cewar ta yi imanin 'yan ta'adda ne, matsorata wadanda basu san abun da suke yi ba, suka kai wannan hari.

Shi ma dai minista a ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya, Dr Mohammed Ali Pate, wanda ya ziyarci wurin ya ce abun ba'a cewa komai.

Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa gininta.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, wanda ya gana da manema labarai akan wannan al'amari ya ce wannan hari ne aka kai ga mutanen suka saudakar da rayuwarsu wajen taimakawa bil-adama.

Shugaban Majalissar Tarayyar Turai, Jerzy Buzek, yayi Allah wadai da harin da aka kai a birnin na Abuja..

Jerzy Buzek ya ce a madadin majalissar Tarayyar Turai, yana mika sakon ta'azziyarsa ga iyalai da 'yan uwa da abokan arziki na mutanen da suka rasa rayukansu a wannan hari.

Ya kara da cewa hari ga ginin Majalissar dinkin duniya, tamkar hari ne ga baki dayan kasashen duniya, domin kuwa Majalissar Dinkin Duniya ta na a Najeriya ne domin taimakawa jama'ar kasar.