An gano gawawwaki a asibitin Libya

Gawawwaki a wani asibitin Libya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gawawwaki a wani asibitin Libya

An gano gawawwakin mutane fiye da dari biyu da suka fara rubewa a wani asibitin da aka daina aiki a cikinsa a Turabulus babban birnin kasar Libya.

Gawawwakin dai sun kunshi maza da mata da na yara a kan gadaje da kuma a harabar asibitin ga jini kuma ya bata ko ina.

Sai dai babu masaniyar ko matattun su wanene, wasu daga cikinsu dai fararen hula ne, wasu mayaka, wasu kuma watakila sojojin haya ne daga wasu kasashen Afirka.