Najeriya za ta hukunta masu harin bam

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da spetan 'yan sanda. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da spetan 'yan sanda.

Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce ba za a yi kasa a guiwa ba, wajen tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a harin da aka kai shalkwatar Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, babban birnin kasar.

A kalla mutane 18 ne suka rasu, a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya kutsa cikin ginin da mota, ya kuma ta da bama baman dake cikin motar.

Tuni dai kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ta yi ikirarin kai harin.

Matsalar tsaro dai na cigaba da zamewa mahukuntan kasar babban kalubale.