Manoma na gudun shirin Bankin duniya

Wani manomi a gonar sa
Image caption Wani manomi a gonar sa

Wasu manoma a jihar Kano dake arewacin Najeriya na dari-dari da karbar shirin nan na tallafawa kananan manoma don bunkasa nomansu.

Shirin tallafin na Bankin duniya ana masa lakabi da noma don riba, kuma shirin na gwaji ne da ake aiwatarwa a jihohi biyar na kasar.

A karkashin shirin ana bukatar manoma su bada rabin kason kudaden da suke bukata na ayyukan noma shi kuma Bankin ya cika sauran rabin kyauta.