CNN ta gano inda Al- Meghrahi yake

Abdel Basset Al- Megrahi
Image caption Abdel Basset Al- Megrahi

Rashin tabbas game da inda Abdel Basset al-Megrahi yake mutumin da aka kama da laifin dana bam a jirgin fasinjan Amurka da ya fadi a Lockerbie ya zo karshe.

Hakan ya biyo bayan wani hoton bidiyo da kafar yada labarai suka nuna dake nuna Almegrahi a gidansa a Turabulus, inda aka sanya masa robon karawa maralafiya iska kuma ana masa karin ruwa.

'yan uwansa dai sunce ya dai na cin abinci kuma wani lokacin ya kanyi dogon suma.

Sakin Al-Meghrahi a shekaru biyu da suka gabata ya fusata kasashen Amurka da Burtaniya.

Sai dai ministan shari'a na majalisar 'yan tawayen Libya, Muhammad Al-Alagi ya ce ba za su mika wani dan Libya ga kasashen yamma ba.