Iyalan Gaddafi sun tsere zuwa Algeria

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kanar Gaddafi

Gwamnatin Algeria ta tabbatar cewa, uwargidan Kanar Gaddafi, Sahiya, da ukku daga cikin 'ya'yansa, sun isa kasar bayan sun tsere daga Libiya.

Wakilin BBC ya ce, da ma Algeria wuri ne da iyalan Gaddafi ka iya zuwa domin neman mafaka, saboda kasar tana da doguwar iyaka da Libiya, kuma har yanzu gwamnatin Algeriar ba ta amince da majalisar wucin gadin Libiya ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Algeriar ta ce, da safiyar yau ne iyalan Gaddafin suka shiga cikin kasar.

Sun hada da babban dansa Muhammad, wanda a lokutan baya aka ce ya kubce daga hannun dakarun tawaye a birnin Tripoli.

Sauran 'ya'yan biyu sune, Hannibal da Aisha.

Majalisar wucin gadin Libiyar, NTC, ta ce, za ta nemi a mika mata iyalan na Kanar Gaddafi.

Wani kakakin NTC ya bayyana matakin da Algeriar ta dauka, na bada mafaka ga iyalan Kanar Gaddafi da cewa, kamar dai hari ne ta kaiwa Libiyar.