An kashe mutane a Guatemala da gangan a shekarun 1940

Guatemala Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kasar Guatemala tamanin ne suka mutu sakamakon gwajin wani magani da akai akansu da gangan a shekarun 1940

Wata hukuma da fadar shugaban kasar Amurka ta kafa tace akalla 'yan Guatemala tamanin da uku ne akayi imanin cewar sun mutu bayan da wasu wasu likitocin Amurka masu bincike, suka saka masu cututtukan da ake samu ta hanyar jima'i da gangan a shekarun 1940.

Daruruwan fursunonin Guatemala, da masu cutar tabin hankali da kuma marayu ne dai suka kamu da cututukan da ake dauka ta hanyar jima'in ba tare da saninsu ba, a wani shiri da gwamnatin Amurkan ta dau nauyin gudanarwa domin yin nazari akan tasirin Penincillim.

Mataimakin shugabankasar Guatemala Rafel Espada, ya fadawa BBC cewa kasarsa zata nemi afuwa saboda rawar data taka a wannan shiri