Jihar Jigawa na fama da ambaliyar ruwa

Jihar kano ma ta samu matsalar ambaliyar ruwa
Image caption Jihar kano ma ta samu matsalar ambaliyar ruwa

A Nigeria, yayin da damuna ta kankama, daruruwan mutane ne kuma ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan a wasu jihohin kasar da suka hada da jihar Jigawa.

Matsalar ta shafi gidaje da gonaki a jihar da ke arewacin kasar, abinda ke janyo fargabar karancin abinci da asarar matsugunai.

Ko a damunar bara ma dai, kusan galibin kananan hukumomin jihar 27 sun gamu da bala'in ambaliyar ruwan.

Tuni ma dai hukumar kai agajin gaggawa ta kasar NEMA ta gargadi mutane akan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar.