Daruruwan fursunoni sun isa Benghazi

Wani gidan yari a Libya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani gidan yari a Libya

Wani jirgin ruwa dauke da daruruwan fursunonin da aka sako daga gidan yarin Libya ya isa Benghazi daga Turabulus.

Dakarun Kanal Gaddafi ne suka kama wasu daga cikinsu a cikin watanni shida da suka gabata, wasu kuwa sun shafe shekaru a gidan yari.

Fursunonin sun bayyana cewa an azabtar da su, inda ake lakada musu duka tare da hana su abinci.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan tawayen ke shirin fafatawa ta karshe a sirte, mahaifar Ghaddafi.