'Gaddafi na barazana ga 'yan Libya'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan tawayen Libya

Majalisar wucin gadin kasar Libiya, NTC, tayi kira ga kungiyar tsaron NATO da kuma kawayenta, da su ci gaba da kai hare-hare ta sama, a kan dakarun Kanar Gaddafi da suka rage.

Da yake magana a lokacin taron ministocin tsaro a kasar Qatar, shugaban NTCn, Mustafa Abdel Jalil, ya ce har yanzu Kanar Gaddafi yana yin barazana, ba wai kawai ga 'yan Libiya ba, a'a, har ma ga duniya baki daya.

Mustafa Abdel Jalil ya ce, yanzu haka da tura ta kai bango, Kanar Gaddafin yana iya aikata wani mugun abun.

Har yanzu dai ba a san inda Gaddafin yake ba, tun bayan da a makon jiya 'yan tawaye suka mamaye birnin Tripoli, inda suka kame hedkwatarsa.