Fiye da mutane 10 sun hallaka a Jos

Jami'an tsaro a Jos
Image caption Jami'an tsaro a Jos

A Najeriya, hukumomin tsaro a jihar Plateau sun ce, mutane goma sha uku ne suka mutu, a tashin hankalin da ya barke jiya a Jos, tsakanin Musulmi da Krista.

To amma alkaluma daga wasu majiyoyi na cewa adadin ya tasamma ashirin.

A nata bangaren kuma, kungiyar Izala, wadda kawanyar da wasu matasa suka yi wa masallacinta na Idi ce ta haddasa tashin hankalin, ta ce kimanin motocinta dari biyu ne kawo yanzu ta gano an kona ko aka lalata, kuma zata bukaci diyya daga hukumomin kasar.

Tuni gwamnatin jihar Filaton ta ce, zata kula da dimbin mutanen da aka jikkata a tashin hankalin.

Tun daga farkon wannan shekarar daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a Jos da kewaye, a tashe tashen hankula masu nasaba da addini da kabilanci da kuma siyasa.