Magoya bayan Julius Malema sun kara da 'yan sanda

Julius Malema Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Julius Malema

A Afirka ta Kudu, 'yan sanda sun yi harbi da gurnetin da ke sa mutum ya kidime, domin tarwatsa masu zanga zanga a birnin Johannesburg, wadanda ke goyon bayan shugaban matasan jam'iyar ANC mai mulki, Julius Malema, mai tsatsauran ra'ayi.

Masu zanga zangar sun rika jifa da duwatsu da kuma kwalabe, sannan suka kona riguna masu dauke da hoton shugaban kasar, Jacob Zuma.

Suna kokari ne su je kusa da hedkwatar jam'iyyar ANCn, inda Julius Malema ke gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa, bisa zargin zubar da mutuncin jam'iyyar.

Wasu 'yan ANCn suna zarginsa da yin zagon kasa ga ikon Jacob Zuma, wanda a shekara mai zuwa zai kara tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar.

Daga baya dai jam'iyyar ANC ta ce, ba za a cigaba da sauraron bahasin a tsakiyar birnin na Johannesburg ba.

Julius Malema ya yi kira ga magoya bayansa da su nuna juriya.