Musulmai a fadin duniya na bikin karamar Sallah

Image caption Sallar Idi a jihar Kano

A ranar Talatace musulmai a fadin duniya su ka gudanar da bukukuwan karamar sallah bayan kammala azumin watan Ramalana.

Bukukwa da dama ne dai ke biyo bayan sallar da aka gudanar da sanyin safiya.

A lokotan bukukuwan sallar dai jama'a kan ziyarci yan uwa da abokan arzuka tare da raba abinci na gargajiya nau'i nau'i dan taya juna murnar sallar.

A Kasar hausa dai hawan sarki shine mafi girma a cikin bukukuwan sallah, inda sarki da hakimansa ke hawa dawaki cikin shiga ta gargajiya tare da kewaya gari dan ganawa da jama'a.

Gwamantin Jihar kano a bana tace babu hawan da za'ayi saboda rashin lafiyar sarkin Kanon.