Tana kasa tana dabo dangane da hawan Sallah a Kano

Jama'ar Kano a filin Idi
Image caption A karon farko cikin kusan shekaru hamsin da hawansa kan karagar mulki, Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya hau keken doki zuwa filin Idi sabanin dokin daya saba hawa bisa al'ada

A Nigeria sanarwar da gwamnatin jihar Kano ta bayar na cewa ba za'a gudanar da hawan sallah ba saboda rashin koshin lafiyar Sarkin Kano'n, bata yiwa jama'ar Kanon da dama harma da wasu masu rike da mukamai a fadar Sarkin Kanon dadi ba.

Gwamnatin Jihar Kanon dai tace sun cimma matsaya da fadar Sarkin, cewa ba za'a gudanar da kowane hawa ba, sai dai wasu majiyoyin fadar sun nuna cewa ba haka maganar take ba, domin kuwa hawa biyu ne kadai aka fasa, amma banda hawan Daushe da ake gudanarwa washe- garin Sallah.

Tuni dama can wasu ke zargin cewa akwai rashin jituwa tsakanin masarautar Kano'n da kuma gwamnatin jahar karkashin jagorancin Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin Jahar ta Kano, Dr. Umar Faruk Jibrill ya shaidawa BBC cewa babu abinda ke tsakanin gwamnatin jahar Kano'n da kuma masarautar Kano'n sai mutunta juna da kuma aiki tare.

BBC tayi kokarin jin ta bakin masarautar Kano'n dangane da wannan batu, to sai dai kuma fadar masarautar Kano'n ta shaidawa BBC cewar bata kaiga cimma matsaya ba akan wannan batu.

Sai dai wata majiya ta shaidawa BBC cewar babu gudu ba- ja -da- baya za'a gudanar da hawan Daushe yau kamar yadda aka saba gani bisa al'ada

A fili dai take cewa Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero bashi da isashiyar lafiya, domin kuwa a karon farko cikin kusan shekaru hamsin da ya yi akan gadon mulki, a bana Sarkin ya hau keken doki ne zuwa filin Idi sabanin dokin daya saba hawa bisa al'ada a duk shekara

Jama'ar da BBC ta zanta da su da dama dai, sun bayyana rashin jin dadinsu game da sanarwar da gwamnatin Kanon ta bayar na dakatar da hawan, suna masu cewar hakan zai ragewa Sallar armashi