Boko Haram na da alaka da Al-qa'ida-SSS

Hakkin mallakar hoto nta
Image caption Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, inda aka kaddamar da harin bam

A Najeriya, Hukumar leken asiri ta SSS ta ce tana tsare da mutane biyu wadanda ake zarginsu da hannu a harin bam din da aka kai ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja a ranar juma'ar da ta gabata.

Hukumar SSS ta ce mutanen da take tsare dasu 'yan kungiyar nan ne na Boko kuma ana tsare da su ne a wani barikin soja.

Hukumar ta ce a yanzu haka tana neman wani mutum wanda ake kira Mamman Nur, ruwa ajallo wanda take zargin cewa yana da alaka da kungiyar al-qa'ida, kuma ya dawo kwananan ne daga kasar Somalia.

Hukumar ta SSS din dai, tayi kira ga al'ummar kasar da su bata goyon bayan wajen samar da bayanan da za su taimaka mata wajen dakile wadanda ke da hannu a harin bam din.

Hukumar har wa yau ta ce mutanen da take tsare dasu na taimaka mata da bayanai kan binciken da take gudanarwa.

Harin bam din da aka kaddamar a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a ranar juma'ar da ta gabata ana ganin harin kunar bakin wake ne, kuma yayi sanadiyar mutumar mutane 23 a yayinda akalla mutane tamanin da daya suka jikkata.

Tuni dai kungiyar nan ta Juma'atul Ahlilsuna lidahwati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram ta dauki alhakin kaddamar da harin.

A watan Yuni ma sai da aka kaddamar da harin kunar bakin wake a Hedkwatar 'yan sanda dake abuja, wanda shima yayi sanadiyar asarar rayuka.