Zimbabwe ta kori Jakadan Libya dake kasar

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An umarci jakadan Libya a Zimbabwe daya bar kasar saboda kona tutar gwamnatin Shugaba Gaddafi da ya yi da kuma daga ta majalisar rikon kwaryar kasar Libyan

Kasar Zimbabwe ta kori jakadan kasar Libya Taha Al -Magrahi, ta kuma bashi sa'oi saba'in da biyu, shida sauran ma'aikatansa su bar kasar.

Matakin yazo ne kwanaki shida bayan da jadakan ya nuna cewar suna goyan bayan gwamnatin wucin gadin kasar Libya, inda kuma ya daga sabuwar tutar majalisar rikon kwaryar kasar Libyan, ya kuma kone tsohuwar tutar gwamnatin kasar Libyan mai launin kore.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe dai, ya jima yana dasawa da Shugaba Gaddafi