'Ya'yan Gaddafi biyu sun yi bayanai masu cin karo da juna

Saif Al Islam daya daga cikin 'ya'yan Kanal Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Saiful Islam yace sun lashi takobin cigaba da yaki har sai abinda hali yayi.

Biyu daga cikin 'ya'yan Kanal Gadafi a Libya sun yi jawabai masu cin karo da juna game da makomar yakin da mahaifinsu yake yi domin kwatarwa kansa iko daga hannun 'yan tawaye

Tashar Al- Arabiya mai watsa labarai da larabci ta ruwaito cewa daya daga cikin 'ya'yan Kanal Gaddafin Sa'adi, yace an bashi hurumin tattaunawa da dakarun dake nuna Kin jinin Kanal Gaddafi a hukumance.

Sa'adi Gaddafi yace yana magana da komandan 'yan adawa domin kawo karshen zubar da jini.

Amma sai dai wani gidan talabijin din mai suna Al- Ra'i yace wani dan Kanal Gaddafin wato Saiful- Islam, ya bayyana masu cewa masu goyan bayan mahaifinsa zasu cigaba da yaki har mutuwarsu.

Saiful- Islam ya kuma yi kira ga 'yan kasar Libyan da su tashi tsaye domin su yaki dakarun 'yan adawa.

Ya kuma bayyana cewar a babban taron da suka gudanar, sun yanke shawarar cewa ba zasu mika kansu ba ga 'yan tawaye, za kuma su yi yaki har sai sun sami nasara.