An hallaka mutane akalla 40 a Jos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rikici a Nigeria

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na cewa mutane kimanin arba'in ne aka hallaka yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka sakamakon wani sabon tashin hankali daya barke a yau a birnin.

Tashin hankalin ya barke ne a Unguwar Dutse Uku,

Wadanda abun ya faru akan idanunsu sun ce al'amarin ya faru ne bayan da wasu mutane da suka labe a cikin wani gini suka harbi wani mutum da ke wucewa, abun da kuma ya sa wasu suka yi yunkurin daukar fansa.

Kawo yanzu dai hukumomi sun ce kura ta lafa, saboda matakan tsaron da suka ce sun tsaurara.

Tashe-tashen hankulla a garin na Jos ya tsayar da al'amurra cik a cikin yan kwanakin nan, yayin da ake ci gaba da zaman zullumi.

Gwamnatin Jihar Pilato ta musanta rahotanni da ke cewar an sanya dokar hana fitar dare.